Adebayo ya ce Baba-Ahmed ya kafa matsayinsa ne bisa abubuwan da ya gani da kuma hulɗar da ya taɓa yi da wasu ’yan siyasa. Ya ce bai dace a haɗa dukkan ’yan takarar adawa cikin irin wannan hukunci ba, musamman waɗanda Baba-Ahmed bai taɓa yin aiki tare da su ba.

1
Da yake magana a shirin News Night na Arise TV, Adebayo ya ce Baba-Ahmed ba shi da isasshen tushe da zai iya tantance ƙwarewarsa wajen jagorantar Najeriya, domin bai taɓa yin aiki tare da shi ba.
Baba-Ahmed, wanda ya kasance mataimakin Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya shirya miƙa mulki. Sai dai ya bayyana cewa, a ganinsa, ’yan siyasar adawa da ke neman maye gurbin Tinubu ba za su iya kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya ba.
Adebayo ya mayar da martani da cewa abubuwan da Baba-Ahmed ya fuskanta a baya a siyasa na iya kasancewa cikin abubuwan da suka gina ra’ayinsa. Ya jaddada cewa bai kamata a haɗa shi cikin ’yan takarar da Baba-Ahmed ke ganin ba za su iya inganta Najeriya ba, yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi.



