A cikin wata sanarwa da shugaban GCAF, Amb. Auwalu Muhd Danlarabawa, ya fitar, ya bayyana cewa lafiyar muhalli na da muhimmiyar rawa wajen kare lafiyar bil鈥檃dama da kuma samun ci gaba mai 蓷orewa. Ya ce samun muhalli mai tsafta, ruwan sha mai inganci, tsaftataccen muhalli da tsarin zubar da shara yadda ya kamata na taimakawa wajen dakile ya蓷uwar cututtuka da inganta rayuwar jama鈥檃.
Shugaban GCAF ya ce kungiyarsa, wadda ke mayar da hankali kan taimakon al鈥檜mma a matakin 茩asa, ta fahimci ala茩ar da ke tsakanin kare muhalli, lafiyar jama鈥檃 da kuma ci gaban al鈥檜mma. Ya bukaci jama鈥檃 da su 蓷auki matakai na zahiri wajen tsaftace muhallinsu, guje wa zubar da shara ba bisa ka鈥檌da ba da kuma kare hanyoyin samun ruwan sha.
Ya kuma shawarci jama鈥檃 da su rungumi dasa bishiyoyi da kuma inganta tsaftar muhalli a gidaje, makarantu, kasuwanni da wuraren ibada. A cewarsa, irin wa蓷annan matakai na taimakawa wajen samar da muhalli mai aminci da rage matsalolin da ke da ala茩a da gur蓳atar muhalli.
Amb. Danlarabawa ya kuma yi kira ga hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su 茩arfafa shirye-shiryen tsaftar muhalli, inganta samar da ruwan sha mai tsafta da wuraren zubar da shara, tare da 茩ara wayar da kan jama鈥檃, musamman a yankunan da ba sa samun isassun ayyukan more rayuwa.
Ya jaddada cewa kare muhalli ba nauyin gwamnati ka蓷ai ba ne, illa nauyin kowa ne. Ya ce ha蓷in gwiwar gwamnati da al鈥檜mma zai taimaka wajen samar da al鈥檜mma mai tsafta, aminci da lafiya ga mutanen yanzu da kuma al鈥檜mmomi masu zuwa.





