Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya jaddada bu茩atar inganta harkar kula da lafiyar yara, musamman wajen samar da damar yin aikin tiyata cikin nasara ga yara masu bu茩atar irin wannan kulawa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin taron shekara-shekara na 25 na 茦ungiyar Likitocin Tiyatar Yara ta Najeriya, APSON, wanda aka gudanar a jihar Bauchi.
A yayin taron, shugaban APSON, Farfesa Roland Osuoji, ya ce 茩ungiyar ta gudanar da ayyukan tiyata kyauta a wasu al鈥檜mmomin jihar kafin taron. Ya ce an duba marasa lafiya 1,537, yayin da aka yi wa daruruwan marasa lafiya tiyata kyauta, ciki har da wasu ayyukan tiyata masu sarkakiya.
Shugaban kwamitin shirya taron, Dakta Kefas John Bwala, ya ce manufar ayyukan ita ce rage yawan yara da ke fama da cututtukan da za a iya magance su ta hanyar tiyata. Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da cewa yara da ke yankunan karkara da wuraren da ba su da isassun cibiyoyin kiwon lafiya sun samu damar samun irin wannan kulawa.





