Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar 蓷aukar matakin ladabtarwa kan shugabannin hukumomin gwamnati da ke karya dokokin bayar da kwangiloli, musamman ta hanyar 茩ara ku蓷in ayyuka fiye da 茩ima.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya bayyana hakan a cikin wata takardar umarni da ya aika wa ministoci, manyan sakatarori da shugabannin hukumomi da kamfanonin gwamnati.
A cikin takardar, Akume ya nuna damuwarsa kan yadda wasu hukumomi ke bayar da kwangiloli ba tare da bin 茩a鈥檌dojin dokar sayen kayayyaki da ayyukan gwamnati ta shekarar 2007 ba, wadda aka yi wa kwaskwarima ta hanyar dokar ku蓷i ta shekarar 2020.
Ya ce irin wannan dabi鈥檃 na haifar da 茩arin ku蓷in kwangiloli fiye da farashin da aka amince da shi, tare da hana wasu 鈥檡an kasuwa damar shiga gasa ta hanyar fifita wasu 鈥檡an kwangila.
Akume ya kuma umarci dukkan hukumomin da ke amfani da ku蓷in gwamnati da su tabbatar da cewa suna bin dokokin da suka shafi bayar da kwangiloli, tare da tuntubar Hukumar Kula da Sayen Kayayyaki ta 茦asa domin samun shawarwari.
Gwamnatin ta kuma garga蓷i shugabannin hukumomin cewa duk wanda aka samu da karya dokokin zai fuskanci hukunci. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake 茩ara nuna damuwa kan yadda ake sarrafa ku蓷a蓷en al鈥檜mma da kuma bu茩atar tabbatar da gaskiya wajen gudanar da ayyukan gwamnati.





