Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce ta gano bayanan masu zaɓe guda 268 da ake zargin suna ɗauke da hotunan da aka samar ta hanyar basirar kwamfuta, wato AI, da kuma wasu kura-kurai.
Daraktan Sashen Fasahar Sadarwa na hukumar, Lawrence Bayode, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels.
Ya ce na’urar tantance bayanan masu zaɓe ta INEC, wato Automated Biometric Identification System, ce ta gano bayanan da ake zargi, kuma hukumar ta fara aikin tantance su da kuma cire waɗanda aka tabbatar ba su dace ba.
Bayode ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da ake zargi sun yi amfani da wata dama ta musamman da aka tanada domin masu nakasar yatsu wajen ƙirƙirar bayanan rajistar da ake bincike a kansu.
Sai dai ya jaddada cewa ba duk hotunan da aka inganta ta amfani da AI ne za a cire ba. Ya ce hotunan mutane na gaskiya da aka yi wa gyara da manhajojin AI za su ci gaba da kasancewa, amma hotunan da aka ƙirƙira gaba ɗaya ta hanyar AI za a cire su idan bincike ya tabbatar da hakan.
Wannan batu ya janyo ce-ce-ku-ce bayan da INEC ta wallafa kundin rajistar masu zaɓe na farko a shafinta a ranar 26 ga Oktoba, inda wasu ’yan Najeriya suka nuna damuwa kan hotuna da bayanan da suke ganin ba su dace ba. Hukumar ta ce kundin ba shi ne na ƙarshe ba, kuma tana sa ran kammala gyare-gyare da tantance bayanan kafin tabbatar da kundin ƙarshe a ranar 15 ga Disamba, 2026.





