Domin 茩ara tabbatar da an gudanar da ayyukan rundunar yadda ya kamata, an kafa kotunan tafi-da-gidanka guda hu蓷u, wa蓷anda suka taimaka wajen hanzarta sauraron shari鈥檕鈥檌n da suka shafi miyagun 茩wayoyi da sauran laifuka. An ce dukkan hukuncin da aka samu cikin wannan lokaci an tabbatar da su ne ta wa蓷annan kotuna.

1
Wannan nasara na nuna yadda 茩udurin siyasa da jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf suka ha蓷u da 茩warewar gudanar da aiki 茩ar茩ashin jagorancin Shugaban Task Force, Barista Muhiyi Magaji Rimingado, wajen mayar da manufofin gwamnati zuwa ingantattun matakai a 茩asa.
Wadannan nasarori ba alkaluma kawai ba ne, domin suna wakiltar 茩arin tsaron unguwanni, ceto matasa daga shaye-shaye da kuma dawo da fata ga iyalai a fadin Jihar Kano. Rundunar ta kuma aika sa茩o ga masu safarar miyagun 茩wayoyi da sauran masu aikata laifuka cewa Kano ba za ta 茩ara zama mafaka ga masu aikata irin wa蓷annan laifuka ba.





