Rahotanni sun ce lamarin ya jawo hankalin jama’a a Kano, musamman saboda shaharar marigayin a kafafen sada zumunta. Mutane da dama sun nuna damuwa tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya kai ga mutuwarsa.

1
Rundunar ’Yan Sandan ta tabbatar da kama mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin, inda ta ce ana ci gaba da bincike. Hukumomin tsaro na ƙoƙarin gano ƙarin bayanai da kuma tantance irin rawar da waɗanda aka kama suka taka kafin a yanke hukunci.
A halin yanzu, ’yan sanda ba su bayyana cikakken bayani kan dalilin kisan ko kuma abin da ya faru kafin harin ba. Rundunar ta ce za ta ci gaba da bincike tare da bin doka wajen tabbatar da adalci ga marigayin da iyalansa.





