An kama wanda ake zargin, mai suna Mustafa Sani, a gidansa da ke Gaida, Abacha Street, Ƙaramar Hukumar Kumbotso, bayan jami’an hukumar sun samu bayanan sirri da ke danganta shi da wata ƙungiyar masu satar babura da ke gudanar da ayyukanta a cikin birnin Kano.

1
Hukumar ta ce binciken ya biyo bayan gano wani babur mai lambar rajista GRR 958 QB daga Jihar Jigawa, wanda aka bi sawunsa har zuwa gidan wanda ake zargin.
A yayin binciken gidan, jami’an NSCDC sun gano wani babur da ake zargin an sace shi ne daga harabar wani asibiti da ke Rijiyar Zaki, kan titin Gwarzo a Kano.
Baya ga baburin, jami’an sun kuma kwato lambobin rajistar babura guda 11, screwdriver guda 6, pliers guda 3 da kuma damin makullan babura guda 3, waɗanda ake zargin suna da alaƙa da baburan da aka sace.
Hukumar ta ce babban wanda ake zargi da jagorantar wannan harkar, mai suna Mansur Nasir Khalil, wanda aka fi sani da “S-Guy”, yana nan a kan gudu, kuma tuni hukumar ta ƙaddamar da farautarsa domin kamo shi da gurfanar da shi a gaban doka.
Kwamandan NSCDC na Jihar Kano, Commandant Mohammed Hassan Agalama IION, ya yaba da ƙoƙarin jami’an da suka gudanar da aikin bisa bayanan sirri, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da ƙara matsa lamba kan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a jihar.

2
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen gano masu aikata laifuka da kuma hana aikata miyagun laifuka.
Hukumar ta tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan wanda aka kama, sannan a gurfanar da shi a gaban kotu bisa tanadin doka bayan kammala binciken.





