Rahotanni daga kafofin watsa labaran Iran sun ce shugabannin biyu sun tattauna kan matsalolin tattalin arziki da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu, tare da duba hanyoyin da za a bi wajen biyan bukatun al’ummar Iran da kuma tabbatar da daidaiton tattalin arzikin ƙasar.
Sun kuma mayar da hankali kan halin da Iran ke ciki sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa ƙasar, da kuma ci gaban ayyukan soji da dabarun da za su taimaka wajen kare muradun ƙasar.

2
Haka kuma, tattaunawar ta shafi samar da makamashi, rage kashe kuɗaɗen gwamnati da ƙarfafa hulɗar tattalin arziki da ƙasashen ketare, yayin da shugabannin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan yadda za a tunkari ƙalubalen da Iran ke fuskanta da kuma makomar ƙasar.


