Rundunar ta ce an gudanar da aikin ne a ranar 31 ga Oktoba, 2026, bayan mayakan 茩ungiyar sun kai hari kan wuraren da sojojin suke zaune a yankin.
Mukaddashin jami鈥檌n hul蓷a da manema labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce dakarun sun yi amfani da 茩arfin sojojin 茩asa da kuma tallafin jiragen ya茩i wajen fatattakar maharan.
Sanarwar ta bayyana cewa wa蓷anda aka kashe sun ha蓷a da Abu Hajara, wanda yake cikin majalisar shawarar 茩ungiyar ta ISWAP, da kuma Abul Walid, wani babban kwamanda da ke da kusanci da Ba Shuwa, wanda rundunar ta bayyana a matsayin babban jagoran 茩ungiyar a yankin.
Sauran wa蓷anda aka kashe sun ha蓷a da mayakan Larabawa guda biyu masu babban matsayi a 茩ungiyar. Rundunar ta ce bayan artabun, dakarunta sun kwato makamai da alburusai da kuma na鈥檜rorin sadarwa daga hannun mayakan.
Wannan nasara ta zo ne kwanaki uku kacal bayan wani samame a Buni Yadi da ke Jihar Yobe, inda rundunar ta ce ta kashe mayakan ISWAP kusan 55, ciki har da wasu kwamandoji. Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare domin raunana 茩ungiyoyin ta鈥檃ddanci da lalata sansanoninsu a yankin Arewa maso Gabas.





