Rundunar 鈥橸an Sandan Jihar Bauchi ta kama wani magidanci mai shekaru 27, Muhammad Garba Ladan, bisa zargin kashe 鈥檡arsa mai watanni hu蓷u, Fatimah Muhammad, a Zirami da ke jihar Bauchi.
Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce mahaifiyar jaririyar ce ta kai 茩ara ranar Alhamis, bayan ta bar 蓷iyarta tana barci, amma lokacin da ta dawo ta same ta ba ta numfashi. An kuma ce mahaifiyar ta ga mijinta yana fitowa daga 蓷akin a lokacin da lamarin ya faru.
An garzaya da jaririyar zuwa Babban Asibitin Azare, inda likita ya tabbatar da mutuwarta, tare da bayyana cewa abin da ya haddasa mutuwar shi ne shake wuya.
Rundunar 鈥檡an sandan ta ce an kama mijin domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta 茩ara da cewa ana ci gaba da bincike kafin a mi茩a wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar domin ci gaba da 蓷aukar matakin da ya dace.





