Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Eitokpah Sunday Akata, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan harin da ya faru a ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a kusa da mahadar Watt Market Roundabout, lokacin da tawagar Peter Obi ke kan hanyarta daga fadar Obong na Calabar zuwa otal ɗin Metropolitan, inda aka shirya gudanar da taron tattaunawar ɗan takarar da jama’
a.
’Yan sanda sun ce wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka, waɗanda ake zargin suna ɗauke da adduna da sanduna, sun fito daga yankin Calabar Road da Clerks Alley suka far wa motocin da ke cikin tawagar.
Harin ya janyo lalacewar gilasan wasu motocin tawagar, yayin da jami’an tsaro da ke yankin suka shiga tsakani domin tarwatsa mutanen da ake zargin. Rundunar ta ce an kama mutum ɗaya, yayin da sauran waɗanda ake zargi suka tsere.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ajo Geoffrey Ordue, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin tare da tabbatar da ainihin yadda harin ya faru.
Rundunar ta kuma ce tana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargi. Ta jaddada cewa kama mutum ba yana nufin an same shi da laifi ba, domin har yanzu yana da damar kare kansa a gaban doka har sai an kammala bincike da shari’a.





