Jarumin ya bayyana cewa ya shiga sabon auren ne da fatan samun dacewa da albarkar wannan lokaci na watan Rabi鈥檜l Awwal, inda ya nemi masoyansa da magoya bayansa da su ci gaba da yi masa addu鈥檃r samun zaman lafiya, fahimtar juna da dorewar aure.
A wani bidiyo da ya wallafa bayan kammala bikin, Zango ya nuna godiyarsa ga Allah, tare da mayar da martani ga masu sukar matakin da ya 蓷auka na sake yin aure.
Jarumin ya ce bai ta蓳a shiga wani aure da niyyar ya rabu da matar ba, yana mai cewa rabuwar da ta faru a auren da ya gabata 茩addara ce da ta faru.
A 茩arshe, Adam A. Zango ya ro茩i masoyansa da su ci gaba da yi masa addu鈥檃 domin Allah Ya ba shi zaman lafiya da kwanciyar hankali a sabon gidansa.





