A cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce duk da cewa kuɗaɗen shiga na gwamnati sun ƙaru, ƙarfin sayen ’yan Najeriya ya ragu. Ya zargi gwamnatin Tinubu da jawo matsalolin hauhawar farashin man fetur, canjin darajar kuɗi da kuma tsadar rayuwa, lamarin da ya ce ya jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin ƙarin talauci.

1
Atiku ya kuma ce abin da gwamnati ke kira gyara ba gyara ba ne, yana mai zargin cewa an ƙara wa ’yan Najeriya wahala tare da bayyana hakan a matsayin nasarar manufofin tattalin arziki. Batun dawo da tallafin man fetur ya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan siyasa yayin da kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ya fara





