Atiku, wanda da kansa ya jagoranci tawagar lauyoyinsa zuwa kotu a Abuja, ya buƙaci kotun ta binciki tare da kwatanta takardun da Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC domin takarar zaɓen 2023 da kuma waɗanda aka gabatar domin zaɓen 2027.
Rahoton ya ce Atiku na son kotun ta tantance bambancin bayanan da ke cikin takardun, musamman dangane da sunayen “Bola Ahmed Tinubu” da “Bola Adekunle Tinubu”, domin gano ko akwai wani saɓani ko kuma rashin daidaito a bayanan da aka gabatar.
Matakin ya sake ƙara zafafa siyasar Najeriya yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027, inda ake ci gaba da samun ce-ce-ku-ce kan cancantar ‘yan takara, sahihancin takardun makaranta da sauran bayanan da ake gabatarwa ga hukumar zaɓe.





