An 茩addamar da kwamitin ne a ranar Talata a Abuja, inda Ministan Ya蓷a Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana kafa kwamitin a matsayin wani muhimmin mataki wajen 茩arfafa gaskiya, ri茩on amana da 茩warewa a harkar talla da sadarwar kasuwanci.
Hajiya Sa鈥檃 Ibrahim, wadda ta shafe shekaru tana aiki a harkar ya蓷a labarai da talla, na cikin mutane biyar da aka na蓷a cikin kwamitin. Mai Shari鈥檃 Cecilia M. A. Olatoregun ce za ta jagoranci kwamitin, yayin da sauran mambobin suka ha蓷a da Musa Ahmed Attah, SAN, Merga Tyowanan Kachina, Esq., da Dr. Ken Onyeali Ikpe.
An kafa kwamitin ne bisa tanadin dokar ARCON ta shekarar 2022, wadda ta bai wa Majalisar Kula da Harkokin Talla ta Najeriya 茩arin ikon sa ido kan masana鈥檃ntar talla tare da samar da tsarin sauraron kararrakin da suka shafi karya dokokin talla da 茩a鈥檌dojin masana鈥檃ntar.
Yayin 茩addamar da kwamitin, Minista Mohammed Idris ya bu茩aci mambobin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, 鈥榶anci da adalci, tare da yanke hukunci bisa hujjoji ba tare da tsoro ko son zuciya ba.
Shi ma Darakta-Janar na ARCON, Olalekan Fadolapo, ya bayyana kafa kwamitin a matsayin wani babban ci gaba wajen tabbatar da bin doka da 茩a鈥檌dojin masana鈥檃ntar talla a Najeriya.
A nata 蓳angaren, shugabar kwamitin, Mai Shari鈥檃 Olatoregun, ta yi al茩awarin gudanar da ayyukan kwamitin cikin gaskiya, adalci da 茩warewa.
Gwamnatin Tarayya ta ce ana sa ran kwamitin zai taimaka wajen samar da ingantacciyar masana鈥檃ntar talla mai bin doka, tare da 茩arfafa 茩ir茩ire-茩ir茩ire, kare amincewar jama鈥檃 da kuma tabbatar da 茩a鈥檌dojin 茩warewa a harkar talla.
Hajiya Sa鈥檃 Ibrahim Ta Shiga Sabon Kwamitin Sauraron Kararrakin Laifukan Talla na Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta na蓷a tsohuwar Darakta-Janar ta gidan talabijin na Abubakar Rimi Television, ARTV Kano, kuma tsohuwar shugabar 茩ungiyar Masu Gidan Rediyo da Talabijin ta Najeriya, BON, Hajiya Sa鈥檃 Ibrahim, cikin mambobin sabon Kwamitin Sauraron Kararrakin Laifukan Talla na Najeriya.

Keep reading
KANO: Gwamnati Na Ci Gaba da Sauye-Sauyen Harkokin Sufuri
Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana ci gaba da 蓷aukar matakai domin inganta harkokin sufuri da rage matsalolin cunkoson ababen hawa a jihar. Matakan na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na samar da ingantaccen tsarin zirga-zirga ga al鈥檜mmar jihar.
Sep 11, 2026 路 1 min read




