Hukumar ta bayyana cewa shagunan sayar da magunguna ba cibiyoyin lafiya ba ne, kuma doka ba ta ba su damar gudanar da ayyukan da suka haɗa da allurar IV ko ƙarin jini ba. Ta ce duk wani chemist ko wurin da ba shi da izini da aka kama yana gudanar da waɗannan ayyuka zai fuskanci rufe wurin nan take.
Mukaddashin Sakataren Hukumar PHIMA, Hajiya Khadijah Hussein Sa’id, ta ce matakin ya yi daidai da manufar gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta “Kano First”, wadda ta sanya kare lafiyar jama’a a matsayin babban abin fifiko. Ta kuma buƙaci jama’a su kai rahoton wuraren da ake gudanar da irin waɗannan ayyuka ba bisa ka’ida ba zuwa ofishin hukumar da ke Magaji Rumfa, tare da gabatar da hujjoji kamar hotuna, rasit ko wata shaida.
Hukumar ta jaddada cewa ƙarin jini da allurar IV ya kamata a gudanar da su ne kawai a asibitocin da aka amince da su, ƙarƙashin kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya, domin kare rayukan jama’a daga haɗarin kamuwa da cututtuka da sauran matsalolin da ka iya tasowa sakamakon rashin bin ƙa’idojin lafiya.




