Da yake gabatar da rahoton a gaban Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Jibril Ismail Falgore, Mataimakin Shugaban Kwamitin, Musa Tahir Hungu, ya ce kwamitin ya gudanar da cikakken bincike kan waɗanda aka gabatar, tare da tabbatar da cancantarsu bisa ilimi da ƙwarewa.

1
Kwamitin ya ba da shawarar tabbatar da Sani Audu Kademi a matsayin Sakataren Gudanarwa na Ƙaramar Hukumar Gaya, Bala Sabo Nuhu na Ƙaramar Hukumar Makoda, da Jamilu Garba Gano a matsayin Sakataren Gudanarwa na Ƙaramar Hukumar Gano.
Musa Tahir Hungu ya ce kwamitin ya duba takardun karatu da cancantar waɗanda aka gabatar, inda ya tabbatar da cewa sun cika ƙa'idojin da ake buƙata domin gudanar da ayyukan.
A ƙarshe, kwamitin ya buƙaci Majalisar ta amince da rahoton tare da ba Gwamnatin Jihar Kano shawarar ta tabbatar da nadin sabbin Sakatarorin Gudanarwar ƙananan hukumomin uku.
Binta Khalid Mohd ta ruwaito cewa Majalisar ta amince da rahoton kwamitin, matakin da ya share hanya ga ci gaba da aiwatar da nadin sabbin jami'an.




