Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya jaddada muhimmancin Cibiyar Nazarin Dabarun Ci Gaba wajen samar da sabbin dabaru da hanyoyin aiki da za su taimaka wajen inganta tsara manufofin gwamnati, hidimar jamaâa da bunÆasa tattalin arzikin Æasa.
Mai Martaba ya bayyana haka ne yayin da ya karÉi tawagar Cibiyar ÆarÆashin jagorancin Janar mai ritaya L. A. Jimoh, wadda ta kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa.
Sarkin ya bayyana cewa cibiyoyin bincike na da muhimmiyar rawa wajen samar da sauyi a harkokin zamantakewa da tattalin arziki, yana mai cewa manufofin da suka dogara da ingantaccen bincike da tunani mai zurfi su ne ginshiÆan samun mafita ga matsalolin da Æasa ke fuskanta.
Ya ce irin waÉannan shirye-shirye na iya taimakawa wajen Æarfafa tattalin arzikin Najeriya, inganta ayyukan gwamnati da kuma samar da hanyoyin da za su amfani alâumma.
Mai Martaba ya kuma tabbatar da cewa Majalisar Masarautar Kano a shirye take ta ba da goyon baya ga duk wani shiri da zai taimaka wajen bunÆasa rayuwar alâumma a Jihar Kano da Najeriya baki Éaya.
Da yake nasa jawabin, shugaban tawagar, Janar mai ritaya L. A. Jimoh, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin gudanar da Kwas na 48 na shekarar 2026 na Cibiyar, tare da neman shawara da albarkar Mai Martaba Sarkin Kano.
Ya bayyana Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaba abin koyi wajen kare kimar alâadu da martabar gargajiya, tare da yi masa fatan samun nasara a ayyukan da ya sanya a gaba.
Janar L. A. Jimoh na tare da Shugaban Maâaikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Sani Wali, Mai Ba Gwamna Shawara ta Musamman kan Harkokin Masarautu, Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, da sauran manyan jamiâan Cibiyar yayin ziyarar.




