Shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci a Najeriya sun amince da 茩ara 茩arfafa zaman tare cikin kwanciyar hankali, fahimtar juna da ha蓷in kai tsakanin mabiya addinan biyu.

1
An cimma matsayar ne yayin wani taron ha蓷in gwiwa da shugabannin addinan suka gudanar a Abuja, biyo bayan ziyarar da Sakatare-Janar na Majalisar 茦oli ta Harkokin Addinin Musulunci ya kai birnin.
Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin ha蓷in kan shugabannin addinai wajen inganta zaman lafiya da kuma rage rikice-rikicen addini da ke iya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar Najeriya.

2
Sun kuma yi kira ga mabiya addinan biyu da su mutunta juna, su guji kalaman da za su iya tayar da rikici, tare da yin amfani da koyarwar addinai wajen 茩arfafa zaman lafiya da ha蓷in kan 茩asa.





