Fadar ta bayyana hakan ne yayin da ta karɓi baƙuncin Mataimakin Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Mista Pedro Sarayo, wanda ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Kano a fadarsa.
A yayin ziyarar, an tattauna kan muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kungiyoyin ƙasa da ƙasa wajen inganta rayuwar al’umma, musamman a fannoni irin su lafiya, ilimi, noma, al’adu da fasahar zamani.

glob hub
Da yake jawabi a madadin Fadar Masarautar Kano, Babban Ɗan Majalisar Masarautar Kano kuma Matawallen Kano, Alhaji Aliyu Ibrahim Matawalle, ya bayyana cewa Fadar Kano na da masaniya kan ayyukan da Tarayyar Turai ke gudanarwa a Najeriya.
Ya ce irin waɗannan shirye-shirye na taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa al’umma da kuma bunƙasa fannoni daban-daban da suka shafi rayuwar ’yan ƙasa.
Alhaji Aliyu Ibrahim Matawalle ya bayyana cewa ayyukan da EU ke tallafawa sun haɗa da shirye-shirye a fannonin lafiya, ilimi, noma da sauran ayyukan da ake aiwatarwa domin inganta jin daɗin al’umma.
Ya ƙara da cewa Masarautar Kano tana maraba da duk wani shiri da zai taimaka wajen kawo ci gaba da inganta rayuwar al’ummar Kano da Najeriya baki ɗaya.
A cewarsa, Majalisar Masarautar Kano a shirye take ta ba da haɗin kai da goyon baya ga shirye-shiryen da aka tsara domin amfanin al’umma, musamman waɗanda za su taimaka wajen inganta rayuwa da samar da damammaki ga matasa da sauran ɓangarorin al’umma.
Ya kuma yi wa tawagar Tarayyar Turai fatan samun kyakkyawar zama a Najeriya da kuma gudanar da ayyukansu cikin nasara.
Tun da farko, shugaban tawagar Tarayyar Turai, Mataimakin Jakadan EU a Najeriya, Mista Pedro Sarayo, ya bayyana cewa ziyarar tasu ta kasance ne domin nuna girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Kano da kuma ƙarfafa dangantakar dake tsakanin Tarayyar Turai da Najeriya.
Mista Sarayo ya ce Tarayyar Turai na da aniyar ci gaba da tallafawa Najeriya a fannoni daban-daban na ci gaban jin ƙai da bunƙasa rayuwar al’umma.
Ya bayyana cewa baya ga fannoni da EU ta dade tana tallafawa, ƙungiyar tana kuma duba wasu sabbin hanyoyi na haɗin gwiwa da suka shafi al’adu, fasahar zamani da harkokin dijital.
A cewarsa, sabbin dabaru da shirye-shiryen na da nufin ƙarfafa damar al’umma da kuma samar da hanyoyin da za su taimaka wajen ci gaban Najeriya.
Mista Sarayo ya kuma nemi goyon bayan Majalisar Masarautar Kano wajen ganin an samu nasarar aiwatar da irin waɗannan shirye-shirye.
Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da hukumomin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da cewa shirye-shiryen ci gaba sun isa ga al’ummomin da aka tsara domin amfanarwa.
Ziyarar ta kuma ba tawagar Tarayyar Turai damar ƙara fahimtar muhimmancin Masarautar Kano da kuma rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa wajen haɗa kan al’umma da kuma tallafawa shirye-shiryen ci gaba.
A yayin ziyarar, an kai tawagar EU rangadin wasu muhimman wurare da fadoji da ke cikin Fadar Mai Martaba Sarkin Kano.
Rangadin ya ba baƙin damar ganin wasu daga cikin wuraren tarihi da ke cikin fadar tare da ƙarin fahimtar tarihin da al'adun Masarautar Kano.
Sarkin Sudan, wanda kuma Hakimin Garko ne, ya raka tawagar Tarayyar Turai yayin rangadin.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara mayar da hankali kan muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da abokan hulɗarta na ƙasa da ƙasa wajen magance matsalolin jin ƙai da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.
Ga Masarautar Kano, irin wannan hulɗa na kuma samar da wata dama ta tattaunawa kan bukatun al’umma da kuma hanyoyin da za a ƙarfafa ayyukan da suka shafi rayuwar jama’a.
A nata ɓangaren, Tarayyar Turai na ci gaba da gudanar da shirye-shirye a Najeriya da suka shafi fannoni daban-daban na ci gaban al’umma, tare da haɗin gwiwar hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Ziyarar Mataimakin Jakadan EU zuwa Fadar Kano ta ƙara jaddada muhimmancin hulɗa tsakanin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma shugabannin gargajiya wajen tallafawa ci gaban al’umma.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun bayyana aniyarsu ta ganin an ƙarfafa haɗin gwiwa, musamman a fannonin da za su amfani al’ummar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Wakilinmu na Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Khalil Ibrahim Yaro, ya ruwaito cewa ziyarar ta ƙare ne bayan gudanar da tattaunawa da rangadin wasu daga cikin muhimman wuraren tarihi da ke cikin Fadar Sarkin Kano.




