Daura, wanda a yanzu yake matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television ranar Litinin.
Ya ce bai yarda da ra’ayin cewa gwamnatin Buhari ita ce mafi muni a tarihin Najeriya ba, yana mai kira ga masu wannan ra’ayi da su duba tarihin mulkin ƙasar daga 1995 zuwa 2023 kafin yanke hukunci.
Daura ya kuma musanta cewa yana cikin wata “cabal” da ake zargin ta yi tasiri a gwamnatin Buhari. Ya ce kasancewarsa kusa da shugaban ƙasa ya samo asali ne daga nauyin aikinsa a matsayin shugaban hukumar leƙen asiri.




