Rahotanni sun ce 鈥榶an bindigar sun kai harin ne da misalin karfe tara da rabi na daren Litinin, inda suka bude wuta kan mutanen da ke zaune a wuraren shakatawa da kuma shagunan da ke kusa. Harin ya jefa mazauna yankin cikin firgici, yayin da wasu suka tsere domin tsira da rayukansu.
Sakataren yada labarai na kungiyar Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai a harin. Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Plateau da jami鈥檃n tsaro da su kara kaimi wajen sintiri da kare al鈥檜mma, tare da gano wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shari鈥檃. Kakakin rundunar 鈥榶an sandan jihar, SP Alfred Alabo, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce har yanzu yana jiran cikakken bayani kan adadin wadanda suka mutu.
A wani lamari na daban a Legas, mutum guda ya mutu yayin da wasu mutum uku suka samu raunuka bayan wani gini mai hawa biyu da ake ginawa ya ruguje a kan titin Akinola, kusa da tashar mota ta Fadeyi, a kan titin Ikorodu. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma鈥檃, 23 ga Oktoba, 2026.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, LASEMA, ta ce ta samu kiran neman agaji da misalin karfe 12 da minti 10 na dare, inda ta tura tawagar ceto zuwa wurin. Masu aikin ceton sun yi amfani da injin tono kasa wajen kokarin fitar da mutanen da suka makale karkashin baraguzan ginin.
A cewar hukumar, an ceto maza uku da ransu zuwa karfe 3 da minti 33 na safiyar ranar, sannan aka gano gawar wani babban mutum a karkashin baraguzan ginin. Wadanda suka tsira sun samu kulawar gaggawa daga jami鈥檃n lafiya kafin a kai su asibiti domin ci gaba da jinya.
Hukumar ta ce har yanzu ba a tabbatar da musabbabin rugujewar ginin ba, yayin da ake sa ran hukumomin da abin ya shafa za su gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa lamarin. An gudanar da aikin ceton ne tare da hadin gwiwar jami鈥檃n kashe gobara, ma鈥檃ikatan lafiya da rundunar 鈥榶an sanda.





