Marigayin na daga cikin manyan masu ri茩e da sarautun gargajiya mafi da蓷ewa a jihar Kano, inda ya shafe shekaru 67 yana ri茩e da sarautarsa, tare da bayar da gudunmawa wajen jagoranci da hidimtawa al'ummar yankinsa.
Gwamna Abba ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai mutunta al'adar gargajiya, wanda tsawon shekarun da ya yi yana kan sarauta suka taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, ha蓷in kai da kiyaye al'adun jihar Kano.
Gwamnan ya ce rasuwar tasa babban rashi ne ga al'ummar Takai, masarautar Kano da Kano baki 蓷aya, musamman duba da 茩warewa da gudunmawar da ya bayar wajen jagoranci na tsawon shekaru da dama.





