Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakatare mai kula da harkokin ma'aikata, Abba A. Dangguguwa ne ya sanya hannu聽a madadin Shugaban Ma鈥檃ikatan Gwamnatin Jihar Kano a ranar 6 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta ce wasu ma鈥檃ikatan gwamnati na cigaba da aiki da gudanar da ayyukan hukuma duk da cewa sun kai lokacin yin ritaya.
Ta kuma umarci ma鈥檃ikatan da suka yi ritaya saboda shekaru ko tsawon lokacin aiki da su mika dukkan takardun hukuma, kadarorin gwamnati ga wadanda ke karkashinsu nan take.
Sanarwar ta kuma gargadi manyan jami鈥檃n gwamnati da su tabbatar da an aiwatar da umarnin ba tare da bata lokaci ba.
Ta ce duk wani jami鈥檌n da aka samu yana taimakawa ko amincewa da cigaba da zaman ma鈥檃ikacin da ya yi ritaya a bakin aiki zai fuskanci matakin ladabtarwa bisa ka鈥檌dojin aikin gwamnati.
Umarnin ya fara aiki nan take.





