Ministan Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa amincewar ta zo ne bayan gwamnatin ta riga ta amince da shirin zamanantar da tashoshin Apapa da Tin Can Island da ke Legas.
Ya ce inganta tashoshin da ke wajen Legas na da nufin rage cunkoson jigilar kaya a tashoshin Legas tare da samar da karin hanyoyin shigar da kaya cikin kasar.
A cewar gwamnatin, aikin zai taimaka wajen kara ingancin sarrafa kaya, rage lokacin da jiragen ruwa ke dauka a tashar da kuma inganta hanyoyin kasuwanci da masana'antu a yankunan da tashoshin suke.
Gwamnatin ta ce shirin na daga cikin babban tsarin bunkasa ababen more rayuwa na ruwa, wanda kuma ya hada da shirye-shiryen gina sabbin tashoshin ruwa masu zurfin gaske a wasu sassan Najeriya.





