Binciken na Platform to Protect Whistleblowers in Africa, PPLAAF, tare da Anti-Corruption Data Collective, ACDC, ya ce daga cikin kadarorin, 152 da darajarsu ta kai kusan dala miliyan 177 an saya ne a lokacin da jami'an da ake alakanta su da kadarorin ke kan mukaman gwamnati.
Rahoton ya kuma ce kadarori 230 daga cikin 284, wato kusan kashi 81 cikin 100, an saya ne ba tare da wani bayyanannen tsarin samun kudin sayen da aka samu a bayanan da aka bincika ba. Jimillar darajar wadannan kadarori ta kai kusan dala miliyan 232.
Sai dai masu binciken sun jaddada cewa alakanta mutum da wata kadara kadai ba ya tabbatar da cewa an samu kudin kadarar ta hanyar sata ko kuma an aikata laifi.
Rahoton ya ce 39 daga cikin mutane 61 da aka bincika an taba zarginsu, gurfanar da su ko yanke musu hukunci kan laifukan cin hanci da rashawa a lokuta daban-daban.
Kungiyoyin sun yi kira ga hukumomin Najeriya da Amurka da su kara bincike kan tushen kudaden da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin, tare da daukar matakin dawo da duk wata kadara da kotu ko bincike ya tabbatar da cewa an samo ta daga kudaden sata.