Barrister Muhuyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai hedikwatar NSCDC ta Jihar Kano, a matsayin wani ɓangare na rangadin sanayya da kwamitin ke gudanarwa tsakanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce matsalolin tsaro da dama da al’umma ke fuskanta suna da alaƙa, kai tsaye ko a kaikaice, da shan miyagun ƙwayoyi, musamman tsakanin matasa. Saboda haka, ya ce magance matsalar na buƙatar haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, jami’an tsaro da kuma al’umma.
A nasa jawabin, Kwamandan NSCDC na Jihar Kano, Commandant Mohammed Hassan Agalama IION, ya tabbatar wa kwamitin cewa hukumar za ta ci gaba da ba shi cikakken goyon baya da haɗin kai wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi, daba da sauran laifuka.
Kwamandan ya ce yaƙi da waɗannan matsaloli nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, yana mai cewa ƙofar NSCDC a Kano a buɗe take sa’o’i 24 a rana, kwana 7 a mako domin haɗin gwiwa da kwamitin.
Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta duba yiwuwar ƙara tura jami’anta domin tallafa wa ayyukan kwamitin, tare da jaddada cewa haɗin gwiwar hukumomin tsaro da sauran hukumomin gwamnati zai taimaka matuƙa wajen rage shan miyagun ƙwayoyi da inganta tsaron al’umma a Kano.
Kwamitin ya kuma yaba da irin goyon bayan da NSCDC ke bayarwa, yayin da hukumar ta sake tabbatar da aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyi, yaƙi da miyagun laifuka da kuma inganta zaman lafiya da tsaro a faɗin Jihar Kano.

2



