Alhaji Aliko Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da wakilin Premier Radio, Abubakar Haruna Galadanchi, inda ya yi bayani kan halin da kasuwar man fetur ke ciki da kuma matakan da kamfanin ke dauka domin rage wa 鈥榶an Najeriya tasirin hauhawar farashin.
Dangote ya ce rikicin da ya barke tsakanin Amurka da Iran da kuma hare-haren da suka shafi muhimman hanyoyin samar da makamashi a yankin sun kara dagula kasuwar man fetur ta duniya.

Dalhatu
A cewarsa, duk da irin wadannan matsalolin da ke faruwa a kasuwannin duniya, matatar Dangote na kokarin ci gaba da samar da man fetur ga kasuwar Najeriya tare da daukar wasu daga cikin kudaden da ake kashewa wajen jigilar kayayyakin domin rage karin kudin da zai hau kan masu saye.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar da matsin lamba kan samar da makamashi a duniya, yayin da hare-hare kan wasu muhimman hanyoyin samar da man fetur da jigilar shi suka kara haddasa damuwa kan wadatar makamashi.
Alhaji Aliko Dangote ya kuma jaddada cewa kamfaninsa zai ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa ana samar wa kasuwar Najeriya isasshen man fetur, duk da kalubalen da ake fuskanta a kasuwannin duniya.
Ya ce matatar Dangote za ta ci gaba da samar da man fetur ga 鈥榶an Najeriya, tare da kokarin rage tasirin matsalolin kasuwar duniya kan farashin da kuma wadatar man fetur a cikin gida.





