Farashin man fetur a wasu gidajen mai a jihar ya tashi daga kusan Naira 860 zuwa tsakanin Naira 1,400 da Naira 1,500 kan kowace lita, lamarin da ya sake 茩ara tsadar sufuri da sauran kayayyaki da ake amfani da su a kullum.
Masu ababen hawa sun ce 茩arin farashin man fetur ya tilasta musu sake duba farashin sufuri domin samun damar biyan ku蓷in man fetur da sauran ku蓷a蓷en gudanar da harkokin sufuri. Hakan kuma na 茩ara sanya fasinjoji fuskantar 茩arin ku蓷in mota a cikin birane da tsakanin garuruwa.

Wasu daga cikin jama鈥檃r da aka zanta da su sun bayyana damuwarsu kan yadda hauhawar farashin man fetur ke shafar kasuwancinsu da kuma ku蓷in da suke kashewa wajen zirga-zirga. Sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su duba hanyoyin rage matsin da hauhawar farashin man fetur ke jefa jama鈥檃 ciki.
Wakilin Premier Radio 102.7 a Jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Dutse, ya zagaya wasu sassan Birnin Dutse domin jin ra鈥檃yin masu ababen hawa da sauran jama鈥檃 kan tasirin sabon 茩arin farashin man fetur da kuma yadda lamarin ke shafar rayuwarsu.





