Jami鈥檌n Hul蓷a da Jama鈥檃 na Rundunar 鈥橸an Sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da Premier Radio a Dutse, inda ya ce an cafke wanda ake zargin ne bayan jami鈥檃n tsaro sun tare wasu 鈥檡an kasuwa a kan hanyarsu ta komawa gida daga Kasuwar Machina da ke Jihar Yobe, zuwa Birniwa a Jihar Jigawa.
A cewar SP Lawan Shiisu Adam, rundunar ta samu nasarar cafke wanda ake zargin shugaban 茩ungiyar ne bayan gudanar da samamen tsaro da kuma bin diddigin bayanan da suka samu dangane da ayyukan 茩ungiyar.
Ya ce ana zargin 茩ungiyar da aikata laifukan fashi da makami da kuma addabar matafiya a wasu hanyoyin da suka ha蓷a yankunan Hadejia, Malam Madori da Birniwa. Rundunar ta ce bincike kan wanda ake zargin da sauran wa蓷anda ake dangantawa da 茩ungiyar na ci gaba.
Rundunar 鈥橸an Sandan Jihar Jigawa ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da sintiri da samame domin kare rayuka da dukiyoyin al鈥檜mma, tare da yin kira ga jama鈥檃 da su ri茩a bai wa jami鈥檃n tsaro bayanan da za su taimaka wajen dakile ayyukan masu aikata laifuka.





