Obi ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawar dimokuraɗiyya na Goodluck Jonathan Foundation na shekarar 2026, da aka gudanar a Bauchi, inda ya ce zaɓen 2027 wata muhimmiyar dama ce ga ’yan ƙasa wajen yanke shawarar alkiblar da Najeriya za ta bi.

1
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su haɗa kai wajen ganin an magance matsalolin da ke jefa ƙasar cikin koma baya, tare da zaɓar shugabanni nagari masu gaskiya da riƙon amana.
Obi ya kuma jaddada buƙatar gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya da adalci, domin samar da sakamakon da ’yan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki za su amince da shi.
Ya yaba wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan kan ci gaba da shirya taron tattaunawar dimokuraɗiyya, yana mai cewa irin waɗannan taruka na taimakawa wajen tattauna hanyoyin ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da ’yancin bangaren shari’a.
Peter Obi ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da kada su amince da shugabanci mara kyau, rashin adalci ko amfani da siyasa wajen karkatar da al’amuran ƙasa, yana mai cewa matakan da ake ɗauka a yau za su iya ƙayyade makomar al’ummomi masu zuwa.




