A cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar a Abuja ranar 26 ga Satumba 2026, ta ce rashin wadataccen albashi, walwalar jami’an tsaro da kuma karancin kayan aiki na daga cikin matsalolin da ke iya jefa wasu jami’ai cikin matsin tattalin arziki.

3
Kungiyar ta bayyana cewa a wasu lokuta jami’an tsaro kan samu motocin aiki, amma su kansu su nemi kudin man fetur, gyara da kuma kula da motocin, baya ga sauran bukatun aiki kamar kayan sawa. A cewar kungiyar, irin wannan yanayi na iya sa wasu jami’ai neman wasu hanyoyin samun kudaden gudanar da aikinsu.
IHRC-RFT ta kuma bayyana cewa ta samu wasu bayanai da ke zargin cewa ana tilasta wa wasu shugabannin matakai ko na jihohi samar da abin da ake kira “return” ga wasu manyan jami’ai da ke sama da su. Kungiyar ta ce akwai zargin cewa a wata hukumar tsaro ana neman makudan kudade daga wasu shugabannin jihohi a kowane wata, daga naira miliyan biyar zuwa miliyan goma, yayin da ake zargin wasu wurare da kaiwa naira miliyan 30.
Sai dai kungiyar ta jaddada cewa ba ta ayyana wadannan zarge-zargen a matsayin tabbatattun laifuka ba, tana mai kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiyar lamarin da kuma gano ko akwai wata hukuma ko jami’an da ke da hannu a irin wannan dabi’a.
IHRC-RFT ta ce ba za a iya samun ingantaccen tsarin tsaro ba idan jami’an da ake sa ran za su kare rayuka da dukiyoyin jama’a suna aiki cikin karancin kayan aiki da matsin tattalin arziki. Ta bukaci gwamnati da hukumomin bincike su dauki batun da muhimmanci, tana mai gargadin cewa rashin magance cin hanci da rashawa na iya raunana tsarin tsaro da kansa.
Sanarwar ta samu sa hannun Amb. Abdullahi Bakoji Adamu, Daraktan Kungiyar na Najeriya, wanda ya bukaci a tabbatar da gaskiyar zarge-zargen ta hanyar bincike kafin daukar matakin da ya dace.





