A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, SC Oluwaseun Abolurin, ya fitar, an ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da sa ido na tsawon kwanaki biyar tare da haɗin gwiwar wani sansanin soji da ke yankin.
Sanarwar ta ce waɗanda ake zargin suna haɗa ruwan ’ya’yan itace mai suna “Barkas Juice”, ta hanyar amfani da ruwa, sinadaran ƙara ƙamshi na wucin gadi, kayan zaƙi, sinadaran canza launi da sauran abubuwan ƙara armashi.

glob hub
Daga cikin abubuwan da jami’an suka kwato akwai babbar mota, kwalaye na ruwan ’ya’yan itacen, injinan sarrafa shi, sinadarai, ganguna da kuma tankin iskar gas.
NSCDC ta ce ana haɗa samfurin ne cikin yanayi marar tsafta, sannan ana rarraba shi zuwa kasuwanni a Legas, Benin City da sauran sassan ƙasar, ta hanyar amfani da wata lambar rajistar NAFDAC da ake zargin na jabu ce: 01-2166L.

Glob Hub
Kwamandan NSCDC na Jihar Legas, Adedotun Keshinro, ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike kan waÉ—anda ake zargin, sannan a gurfanar da su a gaban kotu bisa tanadin doka.





