Ternus, wanda ya shiga Apple a shekarar 2001, ya ta蓳a zama Mataimakin Shugaban Kamfanin mai kula da Hardware Engineering. A tsawon aikinsa, ya taka rawa wajen ha蓳aka wasu manyan kayayyakin Apple da suka ha蓷a da iPhone, iPad, Mac, Apple Watch da AirPods.

1
Nadin nasa ya zo ne a wani muhimmin lokaci ga kamfanin, wanda har yanzu gadon marigayi Steve Jobs, 蓷aya daga cikin wa蓷anda suka kafa Apple, ke da tasiri sosai a al'adun kamfanin. Jobs ya taimaka wajen gina Apple a matsayin kamfanin da ya shahara wajen kirkire-kirkire, sau茩a茩an zane da samar da kayayyakin fasaha na musamman.
Yanzu Ternus zai fuskanci 茩alubalen ci gaba da wannan tarihi, tare da kare nasarorin da Tim Cook ya samu. A lokacin Cook, Apple ta fa蓷a蓷a sosai, inda darajar kamfanin ta tashi daga kusan dala biliyan 350 zuwa sama da dala tiriliyan 4.
Sai dai Ternus ya kar蓳i shugabancin Apple a lokacin da fasahar basirar wucin gadi (AI) ke sauya masana'antar fasaha. Apple na fuskantar matsin lamba daga masu fafatawa kan yadda take tafiyar da shirye-shiryenta na AI.




