Mai Martaba ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mi茩a motocin ga Hakimin Sumaila, Galadiman Daji, Alhaji Aminu Abdullahi Nasidi, da takwaransa na Rimi, Sarkin Sullubawa, Alhaji Idris Sanusi Bayero, a fadarsa.
Sarkin Kano ya bayyana wannan mataki a matsayin ci gaba mai kyau, yana mai cewa motocin za su taimaka matu茩a wajen sau茩a茩a wa hakiman gudanar da ayyukan da aka 蓷ora musu na jagorantar al鈥檜mma.

1
Mai Martaba ya kuma yi kira ga sauran shugabannin siyasa da su yi koyi da irin wannan kyakkyawan aiki, domin tallafa wa shugabannin gargajiya da kuma 茩ara samar da ci gaba a yankunansu.

1
A nasu 蓳angaren, Hakimin Sumaila, Alhaji Aminu Abdullahi Nasidi, da Sarkin Sullubawa, Alhaji Idris Sanusi Bayero, sun gode wa Sanata Kawu Sumaila bisa wannan karamci, tare da jaddada aniyarsu ta ci gaba da tallafa wa duk wani yun茩uri da zai kawo ci gaba ga 茩aramar hukumar Sumaila da Masarautar Kano baki 蓷aya.




