Sarkin ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da 茩ungiyar ta gudanar a Kano, tare da halartar mambobinta daga 茩asashe 26. Ya ce, bisa la鈥檃kari da batun da ke gaban kotu, an dakatar da gudanar da babban za蓳en shugabancin 茩ungiyar har sai kotu ta bayar da izinin ci gaba da aikin.
Wannan mataki ya biyo bayan ziyarar da shugabannin 茩ungiyar daga 茩asashe daban-daban suka kai wa Mai Martaba Sarkin Kano a Fadar Kano, inda suka bayyana goyon bayansu ga jagorancinsa. A yayin ziyarar, shugabannin 茩ungiyar sun ce suna fatan Sarkin zai yi adalci tare da tabbatar da ha蓷in kan al鈥檜mmar Fulani a duniya.

Glob Hub
A nasa jawabin, shugaban 茩ungiyar reshen Ghana ya bayyana cewa sun yi wa Mai Martaba mubaya鈥檃 tare da kyautata masa zato, yana mai cewa suna fatan zai yi amfani da jagorancinsa wajen ha蓷a kan al鈥檜mmar Fulani da kuma kare muradunsu ta hanyar da ta dace.
Da yake jawabi cikin harshen Fulfulde, Mai Martaba Sarkin Kano ya gode wa shugabannin 茩ungiyar bisa yadda suka yi doguwar tafiya zuwa Kano da kuma irin kyakkyawan zato da suka yi masa. Ya kuma jaddada muhimmancin bin doka da mutunta hukuncin kotu wajen warware duk wata takaddama da ta shafi 茩ungiyar.

Glob Hub
A cewar Sarkin, ba za a gudanar da babban za蓳en 茩ungiyar ba har sai an samu izinin kotu, domin tabbatar da cewa duk wani mataki da za a 蓷auka ya kasance cikin tsarin doka. Wannan ya sa aka dakatar da shirin babban taron za蓳en da aka shirya gudanarwa a Kano, har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci ko ta bayar da izinin ci gaba.





