Trump ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake magana da manema labarai a Ofishin Oval na Fadar White House. Ya bayyana harin da aka kai a daren da ya gabata a matsayin mai tsananin 茩arfi, yana mai cewa Amurka a shirye take ta sake kai wa Iran hari a duk lokacin da ta ga bu茩atar hakan.
Trump ya ce Iran na 茩o茩arin sake gina tsarin radar da makamai masu linzami, tare da 茩era wani makami mai linzami da zai iya amfani da shi wajen sanya nakiyoyi a mashigin ruwan Hormuz. Ya ce sojojin Amurka sun lalata wa蓷annan kayan aiki da wuraren da ake ginawa a yankin.
A cewar Trump, hare-haren na baya-bayan nan sun mayar da hankali kan tsarin kariyar sama, radar, kayan aikin sanya nakiyoyi, da wasu muhimman wuraren soji na Iran. Rundunar CENTCOM ta Amurka ta kuma ce hare-haren sun shafi wasu kadarorin sojan ruwa da wuraren sadarwa.
Sai dai rikicin ya sake 茩ara kamari bayan Iran ta mayar da martani da makamai masu linzami da jirage marasa matu茩a kan wasu wuraren da sojojin Amurka suke a yankin. Hakan ya 茩ara haifar da fargabar cewa rikicin na iya fa蓷a蓷a a Gabas ta Tsakiya.




